Shugaba Tinubu ya cire harajin kashi biyar kan ɓangaren sadarwa – NCC

0
Bola-Tinubu-1000x600
Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya soke harajin kaso 5 cikin ɗari na harajin da ake ta cece-kuce a kai kan ayyukan sadarwa, matakin da ke da nufin rage matsin tattalin arziki da masu amfani da kafafen sadarwa a ƙasar ke fuskanta.

Mataimakin shugaban hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC), Aminu Maida ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja.

Maida ya tabbatar da cewa harajin wanda da farko aka dakatar da shi a shekarar 2023—a yanzu an cire shi baki ɗaya a hukumance ƙarƙashin dokokin haraji na kasa da aka yi wa kwaskwarima.

Harajin, wanda ya shafi ayyukan sadarwa na wayar hannu, ya fuskanci suka daga masu ruwa da tsaki, waɗanda suka yi iƙirarin hakan zai ƙara tsadar yin amfani da wayar hannu da duka abubuwan da suka shafi ɓangaren sadarwa a ƙasar.

Shugaba Tinubu ya fara dakatar da harajin ne a watan Yulin 2023 a matsayin wani ɓangare na sake fasalin tsarin kasafin kuɗi da nufin rage tasirin haraji da yawa kan ƴan kasuwa da ɗaukacin ƴan Najeriya.

Amma batun ya sake kunno kai a watan Oktoban 2024, lokacin da Majalisar Dokoki ta ƙasa ta ba da shawarar maido da haraji a matsayin wani ɓangare na manyan matakan samar da kuɗaden shiga, wanda ya haɗa da haraji kan wasanni da ayyukan caca.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *