CHAN 2024: Algeria da Afirka ta Kudu sun tashi canjaras

0
1000061679
Spread the love

Afirka ta Kudu da Aljeriya sun tashi 1-1 a wasan cikin rukuni a gasar kofin ƙasashen Afirka ta ‘yanwasan cikin gida wato CHAN.

Shi ne wasa na biyu da suka gwabza a Rukunin C, wanda ya ƙunshi Guinea da Nijar da Uganda.

Sakamakon ya sa Aljeriya ta ɗare saman teburin rukunin da maki 4, da Uganda ta biyu da maki 3, Guinea ta uku da maki 3, sai kuma Afirka ta Kudun 1.

Nijar ce ta ƙarshe a rukunin maras maki amma wasa ɗaya ta buga.

Ƙaasashen Tanzania da Kenyua da Zanzibar ne ke karɓar baƙuncin gasar ta 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *