Ƴanta’adda sun kashe mutum 127 a hare-hare biyar a Nijar – HRW

0
1000148769
Spread the love

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta duniya, Human Rights Watch, ta ce ƴanbindiga sun kashe sama da mutum 127, ciki har da mazauna kauyuka da musulmai da ke ibada a aƙalla hare-hare biyar a yammacin Tillabéri na Nijar.

An zargi ƙungiyar IS-Sahel da kai hare-haren, ciki har da ƙone gidaje da satar dukiyoyi da dama.

Rahoton ya nuna cewa hare-haren sun saɓa wa dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa kuma ana ganin laifukan yaƙi ne.

Human Rights Watch ta ce hukumomi a Nijar ba su kare fararen hula yadda ya kamata ba, yayin da sojoji ba su mayar da martani ga gargaɗin da aka yi ba, suna watsi da buƙatun mazauna kauyuka don samun kariya.

Shaidun wurare sun ce waɗanda suka kai hare-haren mayaƙan IS-Sahel ne bisa kayan da suka sa da kuma ƙauyukan da aka kai wa hari inda suka yi barazana kafin kai hari suna zargin mutane da haɗin guiwa da sojojin Nijar ko ƙin bin bukatunsu.

Hukumomin Nijar ba su bayar da martani kan rahoton Human Rights Watch ba tukuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *