Ƴanbindiga sun kashe fiye da mutum 30 a Neja

Bayanai daga jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya na cewa wasu ƴanbindiga sun kai hari jihar, inda suka kashe sama da mutum 30 tare da sace wasu da dama.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya aike wa BBC ya ce ƴanbindigar waɗanda ake zargi sun fito daga dajin Kabe sun far wa Kasuwan-Daji da ke ƙauyen Demo da maraicen ranar Asabar, inda suka ƙona kasuwar tare da lalata shaguna da sace kayan abinci.
Sanarwar ta ci gaba da cewa da safiyar yau Lahadi ne haɗin gwiwar tawagar jami’an tsaro suka ziyarci yankin, kasancewar sun samu rahoton harin cikin dare.
