Ƙasashe na neman a tsagaita wuta a yaƙin Sudan

0
1000152778
Spread the love

Amurka da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar sun yi kira da a tsagaita wuta tsawon wata uku a Sudan domin gudanar da ayyukan agaji.

Sun ce hakan zai zama matakin farko na kaiwa ga yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta dindindin a yaƙin basasar.

Haka kuma kasashen biyar sun nemi a samar da tsarin wata tara na mayar da kasar karkashin mulkin dimukuradiyya – tsarin da ba zai kasance karkashin ikon bangarorin da ke yaki da juna ba.

Ba daya daga cikin bangarorin biyu – wato rundunar sojin Sudan ko kuma kungiyar RSF – da ke fada tun watan Afirilu na 2023, da ya ce uffan kan bukatun biyu.

Yakin ya haddasa bala’i mafi girma a duniya ga rayuwar dan’adam – inda ya yi sanadin mutuwar dubban jama’a da raba miliyoyi da muhallinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *