Ƙungiyar AES ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a NIjar

0
1000283118
Spread the love

Gamayyar ƙasashen Sahel da ta ƙunshi ƙasashen da suka haɗa da Mali da Nijar da Burkina Faso sun yi Allah-wadai da harin da aka kai a tashar jirgin sama da ke Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar, inda suka bayyana wadanda suka kai harin a matsayin ‘matsorata’.

A cikin wata sanarwa da shugaban sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore ya fitar ranar Asabar, ƙungiyar ta zargi ƙasashen ƙetare da ke ɗaukar nauyin masu tayar da ƙayar baya a ƙasashensu.

Rahotanni sun ce ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai harin tsakanin daren Laraba zuwa safiyar Alhamis, inda ta ce ya yi matuƙar ɓarna.

Sai dai hukumomin Nijar sun dage cewa an ƙashe maharan giuda 20 tare da kama wasu 11.

Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahamane Tiani ya zargi ƙasashen Faransa da Ivory Coast da Benin da goyon bayan maharan ba tare da ya gabatar da wata shaida ba.

Yayin da ya ke mayar da martani kan zargin, kakakin gwamnatin Benin ya yi watsi da zargin na Tiani a matsayin “maganar banza.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *