Gomnatin Najeriya ta karyata jita-jitan soke jarabawar WAEC da NECO.

Gwamnatin tarayya ta bakin ma’aikatar ilimi ta musanta shirin soke jarabawar WAEC da NECO na shekarar 2025.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktar yada labarai a ma’aikatar, Misis Folasade Boriowo, ta fitar ranar Lahadi a Abuja.
Ta ce ya zama wajibi ma’aikatar ta nesanta kanta daga labaran karya tare da bayyana wa jama’a karin haske.
A cewarta, an samu nasarar kammala jarabawar WAEC na shekarar 2025, inda aka samu wasu kura-kurai da suka faru wadanda ba tare da bata lokaci ba hukumomin da abin ya shafa suka magance su.
Ta kara da cewa ma’aikatar ba ta samu wata sanarwa a hukumance ko rahoto daga WAEC, NECO, ko wata hukumar jarrabawa ba dangane da yadda ake tafka kura-kurai a daya daga cikin jarrabawar.