Antonio Gutteres ya kai ziyarar ta’aziyyan Buhari a ofishin jakadancin Najeriya a New York.

Hoto – MFA.
Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres ya kai ziyarar ta’aziyya ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin New York domin jajanta rasuwar marigayi Muhammadu Buhari.
Yayin ziyarar tasa a ranar Asabar, Mista Guterres ya sanya hannu kan rajistar masu ta’aziyya.
Ya bayyana hidimar da Buhari ya yiwa Najeriya da Afirka a matsayin abubuwan da za a dinga tunawa da shi.