Rundunan ‘yan sandan Adamawa na binciken mutuwar wani matashi a garin Mubi.

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana fara gudanar da bincike kan mutuwar wani matashi mai shekaru 35 mai suna Ibrahim Usman, wanda ake zargin wata tawagar hukumar kwastam ta Najeriya ta harbe shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Laraba.

A cewar Nguroje, jami’an ‘yan sanda reshen yankin da lamarin ya faru ne suka jagoranci tawagar da suka kai ziyara a yankin da lamarin ya faru a wani asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Nguroje ya ci gaba da cewa, “Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a halin yanzu tana gudanar da bincike kan wani mummunan al’amari da ya shafi harbin wani mutum mai suna Ibrahim Usman mai shekaru 35 a garin Muchalla dake karamar hukumar Mubi ta Kudu, da wani harsashi da aka ce wasu ‘yan sintiri na hukumar kwastam ta Najeriya suka harba.

“Al’amarin ya faru ne a ranar 16 ga watan Yuli, 2025, da misalin karfe 4:00 Bayan samun wannan kiran na gaggawa, jami’an ’yan sanda na shiyyar ADSU Gude, karkashin jagorancin DPO, suka kai daukin gaggawa.

“An garzaya da wanda aka kashe zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, FMC Mubi, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.”

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin yayin da hukumar kwastam ta sanar da faruwar lamarin.