Wata motar dakon Man Fetur ta kama da wuta a garin Ibadan.

Spread the love

Wata tankar mai dauke da lita 33,000 na Man Fetur ta kama wuta a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a mahadar Celica, sabon titin Ife Expressway a Ibadan.

Lamarin ya faru ne bayan tankar ta bugi wata mota kirar Prado jeep da wata mota wanda yakai ga motar ta kama da wuta.

Duk da cewa ba a samu asarar rai ba, gobarar ta kuma shafi motar da kuma motar Prado jeep din.

Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Maroof Akinwande ya tabbatar da faruwar lamarin.

Akinwande a cikin wata sanarwa da ya raba wa Manema labarai a ranar Alhamis ya ce an samu rahoton faruwar lamarin ne da misalin karfe 18.27 na ranar Alhamis.