Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari, marigayi shugaban Najeriya.

Tinubu ya sanar da haka ne a taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

“Kafin mu fara addu’o’i domin karrama Buhari, ina sanar da ku cewa mun sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari,” in ji Tinubu.