Zan koma bakin aiki ranar talata duk abinda zai faru – Natasha.

Hoto – @natashaakpoti.
Sanata mai wakiltan Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta sha alwashin ci gaba da aikinta a majalisar dattawa a ranar Talata.
Akpoti-Uduaghan ta ce matakin da zata dauka ya yi daidai da hukuncin da kotu ta yanke.
Ta bayyana hakan ne a wata zantawa da ta yi da ‘yan jarida yayin da ta je mazabarta domin wani shirin horaswa a ranar Asabar.
‘Yar majalisar da ta shiga rudani ta ce dakatarwar ta takaita mata gudanar da ayyukanta na majalisar.
Natasha ta bayyana cewa a hukumance ta sanar da majalisar dattawa a rubuce game da aniyar ta na komawa.
Ta kuma bayyana cewa duk da cece-kucen da ake tafkawa a kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke, za ta ci gaba da zama ranar Talata.