Rikicin Gaza yayi sanadin mutuwar yara kanana sama da dubu 17,000 yayin da dubu 33,000 kuma suka jikkata – UNICEF

Hotunan – UNICEF.
Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce sama da yara 17,000 ne aka kashe, aka kuma jikkata 33,000 a zirin Gaza, inda ƙiyasi ke nuni da cewa aƙalla yara 28 ake kashewa a kowacce rana. UNICEF ya ce matsalar jinƙai a Gaza ta kai ƙololuwa, inda yara da dama ke fama da ƙarancin abinci mai gina jiki da kuma rashin tsaftataciyan ruwan sha.
Tsarin kula da kiwon lafiya a Gaza yana gab da rugujewa saboda yawan marasa lafiya da kuma ƙarancin magunguna da makamashi.
Ba rikicin Gaza kawai ya shafi yara ƙanana a wannan yankin ba, amma suna fuskantar matsalar daƙile hakkokinsu na samun ilimi da kula da lafiya da kuma kariya.
Haka zalika ana kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki mataki don kare yaran da kuma tabbatar da samun damar isar da agajin jinƙai ba tare da cikas ba.
Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce yayin da rikicin ke ci gaba da ta’azzara, dole ne ƙasashen duniya su ɗauki mataki domin daƙile wahalhalun da yaran ke sha.