Likitoci sun bayyana cewa Shugaban America Donald Trump na fama Cutar dake shafan Jijiyoyin jini.

Spread the love

Fadar shugaban Amurka ta White House ta sanar cewa Shugaba Donald Trump na fama da wata matsananciyar lalurar jijiya.

Hakan na zuwa ne bayan kwashe kwanaki ana raɗe-raɗin hakan, bayan wasu hotuna da aka fitar suka nuna wani abu tamkar koɗewa a fatar hannun Trump.

Bayan samun wani kumburi a ƙafafunsa a kwanakin nan “An yi wa Trump binciken lafiya” ciki har da gwajin jijiyoyin jini, kamar yadda sakatariyar ƴaɗa labarun fadar shugaban ƙasar, Karoline Leavitt ta bayyana.

Leavitt ta ce alamun da aka gani a fatar hannun Trump ya faru ne dalilin “koɗewar fata sanadiyyar shan hannu da mutane akai-akai” inda yake yawan shan ƙwayar maganin aspirin, wanda ta ce na daga cikin “matakan da aka saba amfani da su wajen kare cutukan hanyoyin jini”.

Trump mai shekara 79 ya sha yin tutiya game da lafiyarsa, inda yakan bayyana kansa a matsayin “shugaban ƙasa mafi lafiya a tarihin Amurka”.

Cutar da aka gano Trump na fama da ita, wato ‘chronic venous insufficiency’, wadda ke faruwa yawanci a lokacin da jijiyoyin da ke ƙafafu suka gaza harba jini zuwa zuciya, lamarin da ke sanyawa jini ya taru a ƙafa, kuma ya haifar da kumburi.