Kungiyar tarayyar Afrika AU ta dorawa Shugaban kasar Burundi nauyin zama wakilin ta a rikicin yankin Sahel.

Shugaban ƙungiyar tarayyar Afrika kuma shugaban ƙasar Angola João Lourenço, ya sanar da naɗin takwaransa na Burundi, Evariste Ndayishimiye a matsayin manzonsa na musamman a yankin Sahel.
Evariste zai jagoranci sabon yunƙurin diflomasiyya na AU domin tunkarar matsalolin tsaro da na jin ƙai da ke addabar yankin na Sahel.
Manzo na musamman ɗin zai mayar da hankali wajen tattaunawa da hukumomin gwamnatocin ƙasashen , ƙungiyoyi, masu bada shawara, da sauran masu da tsaki, domin samar da tsari da zai haifar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Tsawon shekaru kenan yankin Sahel ke fama da matsalolin tsaro na mayaƙa masu iƙirarin jihadi, musamman a kwanakin nan da aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin wasu ƙasashen yankin. Rashin haɗin kan ƙasashen ya kawo cikas a manufofinsu na yaƙar tsaro da sauran matsalolin da ke addabar yankin.